Amurka

Trump ya soki Pelosi saboda kudin katanga

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka Mark Wilson/Getty Images/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki shugabar Majalisar Wakilan Kasar daga Jam’iyyar Democrat, Nancy Pelosi bayan ta yi watsi da yarjejeniyar shige da fice da kuma gina katanga kan iyakar kasar da Mexico domin kawo karshen matakin rufe ma’aikatun gwamnati na tsawon kwanaki 30.

Talla

Nancy Pelosi ta bayyana shirin Trump na baiwa bakin haure miliyan guda da suka shiga cikin kasar ba bisa ka’ida ba kariya a matsayin wani abu da ba zai yi tasiri ba a fafatukar Trump ta ganin ya samu Dala biliyan 5.7 domin gina katanga akan iyakar Mexico.

A yayin mayar da martani, shugaba Trump ya ce, Pelosi ta nuna dabi’u na rashin tunani, kuma ta wuce gona da iri, in da a yanzu ta zama mai tsattsauran ra’ayi a jam’iyyar Democrat, kamar dai yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Trump ya kuma yi shagube ga Pelosi, in da yake cewa, a maimakon ci gaba da wannan takun sakar, kamata ya yi ta tsaftace titunan birnin San Francisco saboda muninsu. Pelosi dai ‘yar san Francisco ce.

A gefe guda, jama’a da dama da ke gwagarmayar yaki da karbar baki a Amurka suma sun soki shirin na Trump wanda suka bayyana matsayin afuwa ga bakin da ke zama a cikin kasar ba bisa ka’ida ba.

Sai dai Trump din ya ce, sam ba haka bane, babu afuwa a cikin shirin nasa, shekaru 3 ne kawai ya tsawaita a karkashin DACA , wato shirin nan na tsohon shugaban kasar, Barack Obama wanda ke kare kananan yara da suka shiga Amurka amma ba tare da an yi musu takardu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.