Faransa-Google

Faransa ta ci tarar Google Euro miliyan 50

Ana zargi Google da kin bayar da bayanai kan ayyukan da yake gudanarwa a Faransa
Ana zargi Google da kin bayar da bayanai kan ayyukan da yake gudanarwa a Faransa 路透社

Faransa ta ci kamfanin Google tarar Euro miliyan 50 sakamakon samun kamfanin da laifin kin bayar da haske a cikin ayyukan da yake gudanarwa a kasar, kamar dai yadda ka’idojin kungiyar Turai suka tanada.

Talla

Sanarwar da hukumar da ke sa ido domin tabbatar da cikakkiyar kariya ga rumbunan ajiye muhimman bayanan jama’a mai suna CNIL, ta ce ko baya ga laifin kin bayar da haske da kamfanin na Google ya yi, hakazalika ya kuma hana hukumar isa ga wasu bayanan sirri mallakin Google da take son yin bincike a game da su.

Mafi yawa daga cikin bayanan da kamfanin ya hana mahukuntan Faransa yin bincike a kai sun shafi tallace-tallace ne, to sai dai mai magana da yawun Google ya ce sun yi matukar mamaki dangane da matakin, yana mai cewa za su yi nazari domin yanke shawara kan matakin da za su dauka.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne wasu mutane sama da dubu 10 karkashin jagorancin wata kungiya mai suna Quadrature du Net, da kuma wata kungiya mai suna None Of Your Businees suka shigar da wannan kara, bisa zargin kamfanin da aikata ba daidai ba.

Kungiyoyin na zargin kamfanin da boye gaskiya a cikin lamurransa, kuma yin hakan abu ne da ya yi hannun riga da sabuwar doka da kungiyar Turai ta kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI