Tattalin Arziki-Davos

Taron tattalin arziki ya kankama a birnin Davos na Switzerland

Taron dai shi ne karo na 49 wanda kuma ke zuwa dai dai lokacin da hasashe ke nuna yiwuwar karayar tattalin arzikin duniya a wannan shekara.
Taron dai shi ne karo na 49 wanda kuma ke zuwa dai dai lokacin da hasashe ke nuna yiwuwar karayar tattalin arzikin duniya a wannan shekara. REUTERS/Arnd Wiegmann

Wakilan kasashe da na kamfanoni sama da dubu uku ne ke halartar taron tattalin arziki na Birnin Davos da aka fara a yau talata, to sai dai taron na bana bai samu halartar wasu shugabannin kasashen duniya ba.

Talla

Taron wanda shi ne irinsa na 49, an fara shi ne a wani yanayi da Asusun Lamuni na IMF ke gargadi dangane da wasu manyan kalubale da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, lamarin da ya sa aka sauko da hasashen habakar tattalin arzikin shekarar bana zuwa kasa.

A ranar 17 ga watan disambar da ya gabata, shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kare batun kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi a wurin wannan taro, to sai dai sakamakon rikicinsa da bangaren majalisa, wanda ya yi sanadiyyar rufe wasu ma’aikatun gwamnati tsawon wata daya, Trump ko kuma tawagar gwamnatinsa ba za ta halarci taron ba.

Takwaransa na Faransa Emmanuel Macron da ake kallo a matsayin cikakken dan jari hujja ma ya kaurace wa taron sakamakon matsaloli masu nasaba da tattalin arziki a cikin gida Faransa.

Firaministar Birtaniya ma ba za ta halarci taron ba, a daidai lokacin da ta ke kokarin shawo kan ‘yan siyasar kasar game da yarjejeniyar ficewa daga gungun Turai.

Daga nahiyar Afirka ma ana dakon shugabannin kasashe da suka hada da Firaministan Habasha Abiy Ahmed, Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu sai kuma Paul Kagame na Rwanda a matsayinsa na shugaban kungiyar Tarayyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI