Rasha-Amurka

NATO na fargabar warwarewar yarjejeniyar makamai ta Amurka da Rasha

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg Reuters/路透社

Kungiyar tsaro ta NATO ta nuna fargaba kan yadda kasashen Amurka da Rasha suka gaza cimma matsaya dangane da yarjejeniyar kayyade kera muggan makamai, matakin da ta ce babbar barazana ce ga zaman lafiyar duniya.

Talla

Babban sakataren kungiyar tsaron ta NATO Jens Stoltenberg ya ce Rasha ba ta da shirin saduda a shirin ta na kera nau’in makaman masu cin dogon zango ta karkashin kasa wanda ke matsayin barazana ga kasashen nahiyar Turai da su ke takun saka da ita baya ga yin karantsaye ga yarjejeniyar kera muggan makamai.

A cewar Stoltenberg wakilan NATO sun kammala tattaunawa da jami’an Rasha a Brussels ba tare da cimma matsaya ba, matakin da ke nuna cewa Rashan a shirye ta ke yarjejeniyar ta wargaje.

Amurka dai na ci gaba da barazanar janyewa daga yarjejeniyar ranar 2 ga watan Fabarairu yayinda za ta kammala ficewa cikin watanni 6 matukar Rashan ba ta jingine shirin tare da kwance makaman ba.

Sakataren na NATO Stoltenberg ya ce matakin Rasha na kin kwance nau’ikan makaman kirar 9M729 masu cin dogon zango ta karkashin kasa kana kuma masu wuyar ganowa a Na’ura baya ga saukin sarrafawa, ya tilastawa NATO fara shirye-shiryen tunkarar kalubalen da duniya za ta shiga ba tare da yarjejeniyar ba.

A bangare guda dai shugaban Rasha Vladimir Putin na ci gaba da gargadin illar da wargajewar yarjejeniyar ta 1987 za ta haifar ga tsaron duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.