Amurka

Shugaba Trump ya bada damar bude ma'aikatu

Donald Trump Shugaban Amurka na magana dangane da batun yan cin rani daga Mexico
Donald Trump Shugaban Amurka na magana dangane da batun yan cin rani daga Mexico ©REUTERS/Yuri Gripas

Shugaban Amurka Donald Trump ya jinkirta yukunrinsa na gina kantaga a kan iyaka da Mexico,wanda hakan ya kawo karshen matakin rufe ma’aikatun gwamnati na tsawon kwanaki .

Talla

A lokacin da yake jawabi zuwa yan kasar,Shugaban Amurka Donald Trump ya janye matakin tareda daukar alkawalin sake dawowa a kai nan da ranar 15 ga watan Fabrairu shekarar bana.

Janyewar da Shugaba Trump ya yi ,ta soma haifar da suka daga bangaren ya’an jam’iyyar sa, yar majalisa bangaren Republicain Ann Coulter ta zargi Shugaban kasar da nuna gazawa dama dangata shi da tsohon Shugaban kasar Georges Bush da aka yawaita kiran sa a matsayin mai sakaci.

Kusan ma’aikata dubu 800 ne suka rasa albashin su tsawon lokacin da ma’aikatu suka kasance a rufe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.