Isa ga babban shafi
Afghanistan

'Yan Afghanistan na fargabar yarjejeniyar Taliban da Amurka

Wasu daga cikin mayakan Taliban na Afghanistan
Wasu daga cikin mayakan Taliban na Afghanistan REUTERS/Parwiz
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Azima Bashir Aminu
1 Minti

Al’ummar Afghanistan na cike da fargaba game da yarjejeniyar da Taliban ta cimma da Amurka don kawo karshen rikicin kasar na shekaru 17, wadda su ke tsoron juyewarta zuwa sabon rikici.

Talla

A Asabar ne wakilan mayakan Taliban da ke tattaunawar sulhu da Amurka, suka bayyana cimma yarjejeniya, wadda a karkashinta aka tsara janyewar dakarun Amurka daga Afghanistan cikin watanni 18.

Tattaunawar wadda aka shafe kwanaki 6 ana yi tsakanin Taliban da Amurka a kasar Qatar, matukar aka samu nasarar aiwatar da yarjejeniyar, za ta kawo karshen yaki mafi tsawo da Amurka ta shafe shekaru 17 tana fafatawa a tarihinta.

Wani mazaunin garin Kabul, Rajab Ali ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai cewa, yanzu haka tarin fararen hula wadanda su ne suka fi jikkata a hare-haren Taliban tun bayan fara yakar ta da Amrka ta yi a shekarar 2001 na cike da fargaba game da tattaunawar.

A cewar Rajab Ali suna tsoron ka da yarjejeniyar ta zamo tsakanin Taliban da Amurka ne maimakon tsakanin Taliban da al’ummar Afghanistan, sai dai ya ce suna fata ta amfani miliyoyin fararen hula da ke cikin fargaba tsawon shekaru a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.