VENEZUELA

Rasha ta soki Amurka saboda Venezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro Fuente: Reuters.

Rasha ta caccaki matakin Amurka na sanya takunkumi kan kamfanin man fetir na Venezuela da zummar gurgunta gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.

Talla

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya ce, suna goyan bayan matsayar mahukuntan Venezuela da suka bayyana matakin na Amurka a matsayin haramtacce.

Amurka ta dauki matakin ne a ci gaba da kokarin ganin-bayan shugaba Maduro tare kuma da nuna goyon-baya ga shugaban ‘yan adawar Venezuela, Juan Guaido da tuni ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko.

Guaido ya ce, zai karbe iko da kadarorin Venezuela da ke kasashen waje, yayin da sojojin kasar suka bayyana goyan bayansu ga shugaba Maduro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI