Amurka-China

Tilas China ta bude kasuwanninta ga Amurka kafin cimma sulhu - Trump

Tawagar wakilan Amurka da na China yayin tattaunawa a birnin Washington domin sulhunta rikicin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu.
Tawagar wakilan Amurka da na China yayin tattaunawa a birnin Washington domin sulhunta rikicin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu. Reuters

Shugaba Donald Trump, ya ce tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da na China, na gudana kamar yadda ake so, sai dai duk da nasarar, wakilan bangarorin biyu, ba za su cimma wata yarjejeniya ba, har sai ya gana kai tsaye, takaninsa da shugaban China Xi Jinping.

Talla

Wakilan kasashen biyu da ke tattaunawa a birnin Washington sun amince da shirya ganawar shugaba Trump da Xi Jingping a China wani lokaci cikin watan Fabarairu, sai dai har yanzu gwamnatin Amurka ba ta ce komai ba dangane da tsayar da lokacin.

Ganawar wakilan Amurkan da China a wannan makon, ta maida hankali kan kawo karshen rashin fahimtar Junan da ke tsakaninsu kan batutuwan da suka shafi tsarin China na musaya ko kwaikwayon kere-kere, da kuma sassauta yakin fagen kasuwancin da suka shafe watanni suna yi, na kakabawa kayayyakin junansu makudan kudaden haraji, wanda suka dakatar na wucin gadi watanni biyu da suka gabata.

Shugaba Trump ya ce tilas China ta bude kasuwanninta ga masana’antun Amurka, da kuma manomanta, domin saukaka musu shigar da kayan da suke sarrafawa cikin kasar, idan taki amincewa da hakan kuma, babu batun sulhunta rikicin kasuwancin da ke tsakaninsu.

A halin yanzu, wata guda kawai ya rage daga cikin kwanaki 90 na yarjejeniyar tsagaita yakin kasuwancin da ke tsakanin Amurkan da China, idan kuma har wa’adin ya kare ba tare da cimma yarjejeniya ba, Amurka za ta aiwatar da aniyar kakabawa karin kayayyakin da China ke shigarwa kasuwanninta haraji, wadanda darajarsu za ta kai dala biliyan 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.