Isa ga babban shafi
Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabin cika shekaru 2 kan mulki

Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin jawabin hadin kan kasa na cika shekaru biyu kan mulki 5 fabwaru a gaban yan majalisar dokokin kasar dake Capitol.
Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin jawabin hadin kan kasa na cika shekaru biyu kan mulki 5 fabwaru a gaban yan majalisar dokokin kasar dake Capitol. Doug Mills/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Garba Aliyu | Salissou Hamissou
1 min

A cikin jawabinsa na musamman ga alumar kasar Amurka bayan cika shekaru 2 bisa madafun iko, kan halin da kasar ke ciki, Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi Amurkawa da su hada kai sosai don gina kasar maimakon ganin sa a matsayin jagoran wata jamiya.Trump wanda yake jawabin kai tsaye ga mutan kasar ya ce sam shi ba shugaba ne na wata jamiya ko wani bangare ba shugaba ne na kasar Amurka baki daya.

Talla

Donald Trump ya ce shi shugaban kasar Amurka ce baki daya ba na wata jamiya ko bangare ba ne.

Ya ce yana bukatar a kawar da siyasar bangaranci da ramuwar gayya don a hadu a gina kasa.

Ya kare tsatsaurar matakan da ya dauka ta fannin muamullan kasuwanci da kasar China, sannan kuma ya ce zai sake zama na fahimtar juna da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un tsakanin ranar 27 da 28 na wannan wata da muke ciki a Vietnam.

Game da takaddamar gina Katanga tsakanin Amurka da Mexico kuma, Donald Trump ya ce lallai zai ga an yi aikin gina katangar, duk da hawa kujeran naki da wakilan jamiyar Democrat suka yi a kan haka.

Ta fannin kiwon lafiyar jama’a, Donald Trump ya ce ganin irin kokarin da ake yi na samar da maganin cutar sida/ AIDS a kasafin kudaden kasar da zai gabatar, Amurka za ta ga ta yi bankwana da cutar cikin shekaru 10 masu zuwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.