Isa ga babban shafi
Lafiya

Nau'in Tarin Fuka mai bijirewa magani ya haifar da sabon kalubale

Hoton huhun wani mara lafiya da ya kamu da cutar Tarin Fuka.
Hoton huhun wani mara lafiya da ya kamu da cutar Tarin Fuka. Luke MacGregor/Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Asusun yaki da cutukan SIDA, Tarin Fuka da Zazzabin cizon sauro na duniya, ya yi kashedin cewa hatsarin wani nau’in tarin fuka da ke bijire wa magunguna ya kai na cutar Ebola, kuma samun maganinsa na da matukar wahala, wanda dole sai an tashi haikan.

Talla

Asusun, wadda burinsa shi ne kawar da cutuka uku da suka zame wa duniya annoba, wato cuta mai karya garkuwar jiki, tarin fuka da zazzabin cizon sauro, ya shirya kashe dala bilayan 12 kan haka cikin shekaru masu zuwa.

Shugaban asusun, Peter Sands yace kamata yayi duniya ta kadu game da batun tarin fuka mai bijire wa magunguna fiye da yadda take nunawa a halin da ake ciki, inda cutar take bijire wa magunguna da dama masu kashe wadanda suka kamu da ita akalla mutane dubu dari 600 a fadin duniya.

A cikin mutane dubu 600, an yi arzikin warkar da kashi 25, a cewar Sands, wanda a shekarar da ta gabata ya zama shugaban asusun.

Majalisar dinkin duniya dai ta kudiri aniyar kawar da cuta mai karya garkuwar jiki, da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka a shekara ta 2030, amma Sands ya ce gaskiyar lamarin shi ne har yanzu ba a daidata sahu ba game da wannan kudiri.

Tarin fuka, wadda ita ce cuta mai yaduwa mafi hadari a duniya, tana sanadin mutuwar mutane miliyan 1 da dubu 300 duk shekara, wadda hakan ya sa asusun ke kira ga gwamnatoci da su kara azama wajen yaki da wannan cuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.