IMF-Dubai

Tattalin arzikin duniya na fuskantar babban kalubale a bana - IMF

Babbar Manajar asusun bada lamuni na duniya IMF Christine Lagarde
Babbar Manajar asusun bada lamuni na duniya IMF Christine Lagarde Reuters

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya gargadi gwamnatocin kasashe game da kalubalen da ke tunkaro tattalin arzikin duniya a shekarar nan, inda ya ce babu tabbacin za a fuskanci habakar tattalin arziki a bana

Talla

A jawaban da ta gabatar Babbar manajan Asusun na IMF Christine Lagarde ta ce tafiyar hawainiyar da habakar tattalin arziki ke yi a watannin nan manuniya ce ga kalubalen da duniya za ta fuskanta ta fuskar tattalin arziki a bana.

Yayin taron tattalin arzikin da ya gudana a birnin Dubai na hadaddiyar Daular larabawa, taron da ya samu halartar wasu shugabannin na duniya Christine Lagarde ta alakanta batutuwa masu alaka da rikicin kasuwancin karin haraji kan kayaki tsakanin kasashe rashin tabbas kan ficewar Birtaniya daga EU da kuma tsuke bakin aljihu a matsayin dalilan mashassharar tattalin arziki a ban.

Ko a watan jiya dai IMF ta sassauto da hasashenta na bunkasar tatalin arziki a bana daga kashi 3.7 cikin dari zuwa kashi 3.5.

A cewar Legarde rikicin kasuwancin da kuma mayar da martinin haraji tsakanin kasashen Amurka da China na ci gaba da tagayyara tattalin arzikin duniya, la’akari da matsayinsa na mafiya karfin tattalin arziki a kasuwancin duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.