Bakonmu a Yau

Farfesa Lucious Bamaiyi kan taron masana da ke tattauna yadda za a magance cin abinci mai guba ga jama'a

Sauti 03:28
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutum 10 cikin dari a duniya na mutuwa ne sanadiyyar gubar da ke tattare da abincin da al'umma ke ci
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutum 10 cikin dari a duniya na mutuwa ne sanadiyyar gubar da ke tattare da abincin da al'umma ke ci Reuters

Masana daga kasashen duniya 125 na halartar wani taron Majalisar Dinkin Duniya kan yadda za’a dinga tsaftace abinci daga wajen noma har zuwa sarrafa shi domin kare jama’a daga cin abinci mai guba.Majalisar ta ce mutane dubu 400 ke mutuwa kowacce shekara sakamakon cin irin wadannan abincin da aka sanyawa sinadarai masu hadari. Dangane da wannan taro Bashir Ibrahim Idris ya tatatuan da Farfesa Lucious Bamaiyi na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria kuma ga yadda zantawar su ta gudana.