Amurka- Yemen

Majalisar Amurka ta kada kuri'a kan yakin Yemen

Yakin Yemen ya jefa al'ummar kasar cikin bala'in yunwa da durkushewar tattalin arziki
Yakin Yemen ya jefa al'ummar kasar cikin bala'in yunwa da durkushewar tattalin arziki REUTERS/Khaled Abdullah

Majalisar Wakilan Amurka karkashin rinjayen Jam’iyar Democrat, ta amince da wani kudirin doka da zai kawo karshen goyon bayan da Amurkar ke bai wa Saudiya a yakin da take jagoranta a Yemen.

Talla

Da dama daga cikin mambobin Majalisar sun kuma bukaci shugaba Donald Trump da ya tsaurara tsare-tsarensa kan Saudiya.

A karon farko kenan da Majalisar ta goyi bayan kudirin dokar yaki a Yemen, in da mambobinta 248 suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da 177 suka nuna rashin amincewa.

‘Yan jam’iyyar Republican 18 sun bi sahun ‘Yan Democrat 230 wajen amincewa da kudirin na hana sojin Amurka shiga cikin batutuwan yakin Yemen da sunan taimaka wa Saudiya da ake zargi da keta hakkin bil'adama a kasar.

Nan da kwanaki 30 ake saran Majalsar Dattawa za ta kada kuri’arta kan kudirin.

Rikicin Yemen na tsawon shekaru hudu, ya yi sanadiyar mutuwar duban jama’a tare da dankwafar da tattalin arzikin kasar baya ga jefa al’umma cikin bala’in yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.