Amurka-Turai

Trump ya gargadi kasashen Turai kan mayakan IS

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen Turai da su karbi daruruwan mayakan ISIS domin yi musu shari’a bayan dakarun SDF sun cafke su a Syria, yayin da ya yi barazanar sakin su muddin kasashen na Turai suka yi watsi da bukatarsa.

Talla

A wani sako da ya aika a shafinsa na Twitter, shugaba Trump ya ce, Amurka ba ta fatan zura ido kan mayakan na ISIS har su mamaye nahiyar Turai, yana mai cewa, sun yi aiki tukuru tare da kashe makuden kudade, a don haka lokaci ya yi da wasu kasashen za su hubbasa wajen gudanar da aikin da bai fi karfin su ba.

A cewar Trump, Amurka na bukatar kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran kasashen Turai da su karbi mayakan na ISIS da yawansu ya zarce 800, in da ya yi barazanar cewa, matsin lamba ka iya tilasta wa Amurkan sakin wadanda mayakan, yayin da a gefe guda, jami’an gwamnatin Trump suka bayyana fargabarsu game da hadarin da ke tattare da sakin mayakan masu ikirarin jihadi.

Sama da makwanni biyu kenan da gwamnatin Trump ke bukatar wadannan kasashe da su karbi mayakan ‘yan asalin nahiyar Turai, kuma Amurka ta ce, a shirye take ta tasa keyarsu.

Kalaman Mr. Trump sun karfafa tsokacin shugaban Hukumar Leken Asirin Birtaniya wanda ya gargadi cewa, Kungiyar mayakan ISIS na sake kintsa kanta domin kaddamar da wasu sabbin hare-hare a kasashen Turai duk da cewa, dakarun soji sun ci galabar su a Syria.

A cikin watan Disamban da ya gabata ne, Trump ya girgiza manyan aminan Amurka bayan ya sanar da matakinsa na janye kimanin sojojin Amurka dubu 2 daga Syria bisa ikirarinsa na cin galabar mayakan na ISIS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.