Amurka-Turai

Kasashen Turai sun yi watsi da Trump kan IS

Wasu mayakan ISIS da ke tsare a hannun jami'an tsaro
Wasu mayakan ISIS da ke tsare a hannun jami'an tsaro 路透社。

Shugabannin Turai sun yi watsi da kiran Donald Trump da ya bukaci su karbi mayakan ISIS da Amurka ta kama a Syria domin yi musu shari’a a kasashensu na asali da ke Turai. Jamus ce ta fara watsi da bukatar kafin sauran manyan kasashen Turan su bayyana matsayarsu.

Talla

A farkon makon nan shugaba Trump ya yi amfanin da shafinsa na Twitter wajen kira ga Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran kasashen Turai kan cewa su karbi mayakan ISIS sama da 800 da Amurka ta kama a Syria tare da taimakon dakarun kawancenta na Kurdawa, domin yi wa mayakan shari’a a kasashensu na asali.

Bukatar Trump ta zo ne a dai dai lokacin da nahiyar Turai ke fargabar zai yi wahala dakarun Kurdawa su iya ci gaba da tsare 'yan kungiyar ta ISIS da suka kama, idan Amurka ta kammala janye dakarunta dubu 2000 da ke tallafa musu a Syria, idan har Turkiya ta kaddamar da farmaki akansu, kamar yadda ta yi barazana.

Tuni Jamus ta ce, abu ne mai wahala a shirya maida kamammun mayakan na ISIS gida cikin gajeren lokaci, yayin da Birtaniya ta ce, a yi wa mayakan na ISIS shari’a a in da aka kama su, matsayar da sauran kasashen Turai suka amince da ita, ciki har da Faransa, wadda yawan ‘yan kasarta da ke cikin mayakan na ISIS da aka kama suka fi na takwarorinta a Turai yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI