Syria-Faransa

Mashiryin harin Paris na 2015 na cikin mayakan IS da aka kashe a Syria

Clain dan asalin kasar Faransa shi ne ya karanta sanarwar daukar nauyin harin watan Nuwamban 2015 da IS ta hallaka fiye da mutane 200 a birnin Paris
Clain dan asalin kasar Faransa shi ne ya karanta sanarwar daukar nauyin harin watan Nuwamban 2015 da IS ta hallaka fiye da mutane 200 a birnin Paris DELIL SOULEIMAN / AFP

Wata Majiyar tsaro a Faransa ta sanar da kisan jagoran maharan birnin Paris na shekarar 2015 Fabian Clain da ya koma yaki a Syria karkashin kungiyar IS.

Talla

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da kisan Fabien Clain wanda ya koma Syria tun cikin watan Maris na shekarar 2015, inda ta ce an hallaka shi ne a marika ta karshe da ke karkashin ikon mayakan na IS a Syria bayan farmakin mayakan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka don kammala kwace iko da yankunan da basa hannun ikon gwamnati.

Clain dan asalin kasar Faransa da ya karbi addinin Islama a 1990, ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa ayyukan ta’addanci a Iraqi cikin shekarar 2009, haka zalika shi ne ya karanta sanarwar daukar nauyin harin birnin Paris na 2015 wanda ya hallaka mutane 129.

Tun bayan karbar musuluncinsa Clain wanda aka fi sani da Abu Adam Al-Faransi ya fada cikin kungiyoyin tsaurin addini inda har kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari, sakamakon yadda aka same shi da hannun a tallafawa ayyukan ta’addanci.

Kawo yanzu dai ma’aikatun harkokin wajen Faransa da na tsaro ba su tabbatar da kisan Clain ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.