Masar-Turai

Kasashen Larabawa da Turai za su yaki ta'addanci da kaurar baki

Taron wanda ya gudana a Masar ya samu halartar shugabannin Nahiyar Turai da na yankin Larabawa
Taron wanda ya gudana a Masar ya samu halartar shugabannin Nahiyar Turai da na yankin Larabawa MOHAMED EL-SHAHED / AFP

Shugabannin Kasashen Turai da na Larabawa sun kammala taronsu na kwanaki biyu a Masar inda suka yi shelar bude wani sabon babin dangantakar da ta shafi yaki da ta’addanci da kaurar baki.

Talla

Shugabannin kusan 40 da suka halarci taron da ya gudana a Sharm el Sheikh sun bayyana cewar kalubalen da su ke fuskanta sun yi kama da juna, saboda haka sun kudiri aniyar yin aiki tare domin inganta yankunan su kamar yadda dokokin duniya su ka tanada.

Shugaban kasar Masar Abdel Fatah al Sisi da ya jagoranci taron ya bayyana wasu matsalolin da su ke fuskanta da suka hada da yaki da ta’addanci da kaurar baki da tattalin arziki da kuma tashin hankali a kasashen Yemen da Syria da Libya da kuma rikici tsakanin Israila da Falasdinawa.

Shugaban kungiyar Turai Jean Claude Juncker ya ce banbancin da ke tsakanin kasashen kan cin zarafin Bil Adama ba zai hana su kulla dangantaka mai karfi ba.

Babbar jami’ar diflomasiyar kasashen Turai Federico Mogherini ta ce bangarorin biyu na da matsayi guda kan yaki da ta’addanci da dakile daukar matasa zuwa shiga ayyukan da suka shafe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.