Yemen-MDD

Agajin kayan abincin Majalisar Dinkin Duniya sun isa Yemen

Isar da kayan abincin na zuwa ne bayan wata yarjejeniya da aka cimma a Sweden a ranar 17 ga watan nan na Fabairu
Isar da kayan abincin na zuwa ne bayan wata yarjejeniya da aka cimma a Sweden a ranar 17 ga watan nan na Fabairu REUTERS/Luisa Gonzalez

Majalisar Dinkin Duniya ta isar da tarin abincin agaji kan iyakar Yemen domin ciyar da miliyoyin al’ummar kasar da ke cikin mawuyacin hali. A karon farko kenan da ake isar da irin wannan kayan agajin abincin tun watan Satumban da ya gabata.

Talla

Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya shaidawa taron manema labari a birnin Geneva cewa, an isar da kayayyakin abincin agajin zuwa Yemen, abin da ya bayyana da labari mai dadin ji.

Mai magana da yawun Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce, isar da abincin a kusa da yammacin birnin Hodeida, wani gwajin dafi ne, yana mai cewa a karon farko tun watan Satumban da ya gabata, sun samu nasarar isar da ton dubu 51 na hatsi a yankin tekun Maliya, abinda zai wadatar da sama da mutane miliyan 3.7 a cikin wata guda.

Isar da kayan abincin na zuwa ne bayan wata yarjejeniya da aka cimma a Sweden a ranar 17 ga watan nan na Fabairu, in da bangarorin da ke rikici da juna a Yemen suka amince su kwashe mayakansu daga tashar birnin Hodeidah da sauran wuraren da ke da muhimmanci ta fuskar bayar da kayan agaji ga jama’ar kasar.

Yakin basasar Yemen ya kazanta tun watan Maris din shekarar 2015, lokacin da shugaba Abedrabbo Mansour Hadi ya tsere zuwa Saudiya, yayin da rundunar hada da Saudiyar ke jagoranta ta shiga cikin yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI