India-Pakistan

Amurka ta bukaci sanin nau'in makamin da Pakistan ta kakkabo jirgin India

Kasar Amurka ta bukaci karin bayani daga Pakistan kan ko kasar ta yi amfani da nau’in kananan jirage kirar F-16 samfurin Amurkan wajen kakkabo jiragen yakin India, matakain da Amurkan ke cewa idan har ya tabbata hakan ne, Pakistan ta karya yarjejeniyar cikinin jiragen yakin daga Washington.

Wasu sojin Pakistan kenan tsaye gab da baraguzan jirgin yakin India da kasar ta kakkabo gab da yankin Kashmir da kasashen biyu ke takaddama akansa
Wasu sojin Pakistan kenan tsaye gab da baraguzan jirgin yakin India da kasar ta kakkabo gab da yankin Kashmir da kasashen biyu ke takaddama akansa STR/AFP/Getty Images
Talla

Tun kafin yanzu dai Pakistan ta fito ta bayyana cewa ba ta yi amfani da nau’in jirgin na F-16 kirar Amurka wajen kakkabo jiragen na India ba, sai dai kawai ta yi amfani da wani salon yaki ne na kare kai daga hare-hare.

Sai dai duk da hakan Amurkan ta kara nanata bukatar cikakkun bayanai kan salon da Pakistan ta yi amfani dasu wajen kakkabo da jiragen na India a makon jiya, bayan tsananta rikici tsakanin kasashen na India da Pakistan makwabtan juna, kuma mamallaka makaman nukiliya.

Ofishin Jakadancin Amurkan da ke birnin Islamabad ya ce tabbas su na bukatar cikakken karin bayani daga ma'aikatar tsaron Pakistan don tabbatar da cewa kasar ba ta karya yarjejeniyar da ta kulla da Amurkan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI