Syria-Amurka

Ba a kammala murkushe IS a Syria ba - Sojin Amurka

Motocin Sojin Amurka da ke yakar marika ta karshe a hannun mayakan IS
Motocin Sojin Amurka da ke yakar marika ta karshe a hannun mayakan IS Delil SOULEIMAN / AFP

Wani Kwamnadan sojin Amurka da ke kula da Gabas ta Tsakiya, Janar Joseph Votel, ya ce har yanzu ba a kammala murkushe mayakan kungiyar IS a Syria ba, saboda haka ya na gargadin kawayen Amurka da kada su yi sakaci da kungiyar.

Talla

Janar Votel ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a gaban 'Yan Majalisun Amurka, inda ya ke cewar kawar da daular mayakan ba karamar nasara ba ce, amma kuma har yanzu akwai sauran birbidin su, tare da wasu 'Yan ta’adda.

Kwamnadan wanda ake saran ya yi ritaya a cikin watanni masu zuwa, ya shaidawa 'Yan Majalisun cewar, yakin da za’a fuskanta nan gaba shi ne na masu goyawa mayakan baya da kuma masu daukar nauyin su.

A karshen shekarar bara ne dai shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da aniyar janye dakarunsa daga Syrian a yakin da su ke da mayakan na IS, inda ya ce Turkiya kadai za ta iya kammala kakkabe mayakan da suka yi saura.

Sai dai sauran kasashen da ke da dakaru a kasar ta Syria karkashin rundunar hadaka da Amurkan ke jagoranta da suka kunshi Faransa da Jamus har yanzu na da shakku kan matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.