Amuka-Yahudawa

Trump ya caccaki 'yan Majalisar wakilai kan kyamar Yahudawa

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Carlos Barria

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kakkausar suka kan ‘yan Jam’iyyar Democrats wadanda ya kira da masu nuna kyamar Isra’ila da yahudawa bayan kalaman ‘yar Majalisa Ilham Omar da ya kai ga tafka muhawara a Majalisar kasar karkashin jagorancin Nancy Pelosi.

Talla

Shugaban Amurka Donald Trump wanda dama ya na fuskantar takun saka da Majalisar bayan daukar matakin hana shi kudin ginin Katanga tsakanin iyakar kasar da Mexico, ya ce yanzu ya fito fili cewa Majalisar ta karkata ne kai tsaye ga kyamar Isra’ila da Yahudawa.

Trump wanda ya bayyana mahawarar da aka tafka a Majalisar Jiya, bayan kalaman na Ilham Omar da abin kunya, ya ce Jam’iyyar Democract ba komi bace face jam’iyyar kyamar Yahudawa.

Kalaman na Trump dan Jam’iyyar Republican na zuwa ne kwana guda bayan takaddama kan dokar haramta kyamar yahudawan da ta gudana a Majalisar wakilan kasar, inda ‘yar Majalisa Ilham Omar musulma ta kalubalanci dokar matakin da ya kai ga rarrabuwar kai tsakanin mambobin Majalisar da ke da rinjayen ‘yan Jam’iyyar Democrats.

Shugaban na Amurka Donald Trump dai kai tsaye na nuna goyon baya ga Isra’ila da Yahudawa, inda ko a bara ya tabbatar da aniyarsa ta mayar da Qudus babban birnin Isr’ila, duk da takaddamar da ke tsakanin kasar da Yankin Falasdinu kan mallakar birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI