Venezuela-Maduro

Maduro da Guaido sun kira babbar zanga-zanga a Venezuela

Dubban Yan kasar Venezuela ake saran yau su sake gudanar da zanga zanga kan halin da kasar ke ciki, yayin da shugaban yan adawa Juan Guaido ke cigaba da matsawa shugaba Nicolas Maduro lamba, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar katsewar wutar lantarki.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro Miraflores Palace/Handout via REUTERS
Talla

Su dai shugabannin biyu, wato Nicolas Maduro mai mulkin kasar da Juan Guaido, shugaban yan adawa sun bukaci magoya bayan su da su yi fitar dango domin cika titunan biranen kasar.

Guaido ya rubuta ta kafar twitter cewar, ya na bukatar magoya bayan sa da su mamaye birnin Caracas domin adawa da haramtacciyar gwamnatin da cin hanci da rashawa ya dabaibaye ta, kana kuma ta kasa biya musu bukatun su.

Shugaban Majalisar dokokin kasar ya ce idan sun fito zanga zangar yau, ba za su koma gida ba har sai sun cimma biyan bukatun kan su.

Shi kuwa shugaba Nicolas Maduro ya bukaci magoya bayan sa ne da su fito domin yaki da yan jari hujja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI