Amurka-Taliban

An samu gagarumar nasara a tattaunawarmu da Taliban -Amurka

Hoton taron Wakilan Amurka da na Taliban a Qatar
Hoton taron Wakilan Amurka da na Taliban a Qatar Al Arabia

Wakilan Kasar Amurka da na Kungiyar Taliban sun kammala taron su a Doha da ke kasar Qatar, inda Jakadan Amurka na musamman Zalmay Khalizad ke cewar an samu gagarumar cigaba a taron.

Talla

Khalizad ya aike da sako ta kafar twitter cewar, yanzu suka kamala taro mai tsayi tsakanin su da wakilan kungiyar Taliban, kuma an samu karuwar bukatar rungumar zaman lafiya, yayin da kowanne bangare ke bukatar ganin an kawo karshen yakin da ake yi a Afghanistan.

Jakadan ya ce mataki na gaba shi ne tattaunawa a Washington, duk da ya ke babu wata yarjejeniya har sai an kammala amincewa da sharadodin da aka gindaya.

Shi ma kakakin kungiyar Taliban ya tabbatar da cewar an samu cigaba a tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.