Amurka

Har Amurka da Najeriya sun hana amfani da Boeing 737 Max 8

Jirgin American Airlines, kiar Boeing 737 Max 8 e Max 9
Jirgin American Airlines, kiar Boeing 737 Max 8 e Max 9 REUTERS/Shannon Stapleton/File Photo

Amurka ta bi sahun sauran kasashen duniya ta hanyar daukar matakin hana jiragen sama kirar Boeing 737 MAX 8 da MAX 9 gudanar da zirga-zirga a cikin kasar.

Talla

Shugaba Donald Trump da kansa ne ya bayar da wannan umurni, biyo bayan hatsarin da irin wannan jirgi mallakin Ethiopian Airlines ya yi a karshen makon jiya tare da haddasa asarar rayukan mutane 157.

Trump ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar Amurkawa da kuma sauran jama’ar duniya na da muhimmanci, to sai dai manazarta na ganin cewa dole ne Amurka ta dauki matakin domin kare martabar kamfanin na Boeing da ake kerawa a kasar.

Kafin nan, kasashen duniya da dama ne suka dauki irin wannan mataki, da suka hada da na yankin Turai, China, Indonesia, Canada, Lebanon, Masar da kuma Najeriya.

Masana sun bukaci a bincike sahihancin wannan jirgi, sakamakon rahotannin tangarda tun wajen kera shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI