Bakonmu a Yau

Bawa Kaumi shugaban cibiyar al’adu ta hadin giwawar Faransa da Nijar kan makon raya harshen Faransanci

Sauti 02:58
Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ludovic Marin/Pool/REUTERS

Daga yau Litinin an shiga makon raya harshen Faransanci a duniya, harshen da ke matsayin daya daga cikin manyan harsuna da ake amfani da su wajen gudanar da mu’amala irin ta yau da kullum da kullum ko kuma a hukumance.Kan wannan AbdoulKareem Ibrahim Shikal ya tattauna da shugaban cibiyar yada al’adu ta hadin giwawa tsakanin Faransa da Nijar wato CCFN da ke Zinder, Bawa Kaumi, wanda da farko ya fara yin bayani dangane da tarihin kafa kungiyar kasashe masu ma’amala da harshen na Faransanci wato Francophonie.