Netherlands

'Yan sandan Holland na laluben maharin Utrecht da ya hallaka mutum 1

Hukumomin Kasar Nertherlands sun ce su na farautar wani mutum da aka Haifa a Turkiya kan harin da aka kai Utrecht yau wanda yayi sanadiyar hallaka mutum guda.

Tuni dai mahukuntan kasar suka bayyana harin da na ta'addanci
Tuni dai mahukuntan kasar suka bayyana harin da na ta'addanci REUTERS/Piroschka van de Wouw
Talla

'Yan Sandan sun sanar da jama’ar birnin cewar, sun sanya ido kan mutumin Gokman Tanis mai shekaru 37 dangane da harin da aka kai yau da safe.

Rahotanni sun ce dan bindigar ya bude wuta kan jama’a inda ya kashe mutum guda, ya kuma jikkata wasu da dama.

Firaminista Mark Rutte ya bayyana harin wanda ke zuwa kwanaki kafin zaben kasar a matsayin abin tayar da hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI