Isa ga babban shafi
Lafiya

Binciken masana ya gano magungunan cizon maciji

Masanan sun ce cikin sauri akan iya magance dafin maciji idan an san nau'in da ya yi cizon
Masanan sun ce cikin sauri akan iya magance dafin maciji idan an san nau'in da ya yi cizon google.com
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Wani Binciken masana ya yi bayani kan yadda jama’a za su kaucewa cizon macizai musamman a yankunan da ake fama da matsalar su sosai.

Talla

Masanan da suka fito daga kungiyar ‘Doctors Without Borders’ da ‘Centre for Disease Control and Prevention’ da ‘Health Action International’ da kuma ‘Bio-Ken Research Centre’, sun bayyana hanyoyin da suka hada da kaucewa razana macizan da sanya takalmin leda a inda ake fama da matsalar su da kuma amfani da fitila wajen tafiya da daddare.

Masanan sun ce sau tari macizai kan kutsa kai ciin dakuna wajen farauta, kana kuma su samu mafaka a ciki, saboda haka ya na da kyau mutane su dinga amfani da fitila wajen haska dakunan su kafin kwanciya ko kuma amfani da gidan sauro mai dauke da magani.

Masanan sun bukaci wadanda macizai suka sara da suyi kokarin gane irin macijin, domin hakan kan taimaka wajen bada maganin da ya dace.

Masanan sun kuma ja kunnen jama’a wajen kokarin kama macijin da ya cije su, ko yanke wurin, ko kuma kokarin zuko gubar sarar ko shan giya ko kuma kofi a matsayin magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.