Somalia

Sojin Amurka sun kashe fararen hula a Somalia- Amnesty

Hoton jiragen yakin Amurka a Somalia
Hoton jiragen yakin Amurka a Somalia World Defence Forum/Facebook

Kungiyar Amnesty International ta zargi dakarun Amurka da kisan fararen hula a Somalia ta hanyar hare-haren jiragen sama a dai dai lokacin da alkaluman mamatan ke ci gaba da keruwa. Sai dai rundunar sojin Amurka ta musanta zargin kisan fararen hular, tana mai cewa, mayakan al-Shebab ta hallaka a kasar.

Talla

Rundunar Sojin Amurka ta ce, ta kai hare-haren sama har sau 110 da jirage marasa matuka a cikin shekaru biyu da suka gaba a Somalia, abinda ya kashe mutane fiye da 800, amma rundunar ta ce, ‘yan ta’adda zalla ta hallaka.

Sai dai a wani binciken kwa-kwaf da ta gudanar kan hare-haren sama guda biyar, Amnesty International ta ce, akalla fararen hula 14 aka kashe, kuma ana fargabar adadin mamatan ka iya zarce haka idan aka kwatanta da jummular hare-haren na sojin Amurka.

A cikin rahoton nata mai taken yakin boye na Amurka a Somalia, Amnesty ta ce, harin ya karya dokokin kasa da kasa, lamarin da ka iya zama laifukan yaki.

Amnesty ta tattauna da mutane 150 da suka hada da shaidun gani da ido da iyalan wadanda aka hallaka har ma da kwararru a harkar tsaro.

Amnesty ta yi amfani da hotunan tauraron dan adam wajen gudanar da bincikenta kan kashe fararen hular.

Amurka dai na cewa, jiragen samanta marasa matuka na kai harin ne kan mayakan Al-Shebab masu alaka da Al-Qaeda, yayinda Amnesty ta ce, tun watan Afrilun shekarar 2017, Amurka ta zafafa hare-haren saman a Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI