Halin da ake ciki a New Zealand bayan ta'addancin da aka yiwa Musulmi

Sauti 20:06
Fira Ministan kasar New Zealand Jacinda Arden.
Fira Ministan kasar New Zealand Jacinda Arden. REUTERS

Shirin Mu Zagaya Duniya dake bitar wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka auku a makon da ya gabata, yayi waiwaye kan bikin zagayowar makon girmama harshen Faransanci da aka saba yi duk shekara. Zalika shirin ya leka kasar New Zealand don jin inda aka kwana dangane da matakan da hukumomin  kasar ke dauka bayan kisan gillar da wani dan ta'adda ya yiwa Musulmi 50 a wasu Masalattan Juma'a.