Amurka- Korea ta Arewa

Trump ya janye wa Korea ta Arewa takunkumai

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jon-un da Donald Trump na Amurka
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jon-un da Donald Trump na Amurka 路透社

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da soke takunkuman da Hukumar Kula da Asusun kasar ta kakaba wa Korea ta Arewa da zummar kuntata mata a matakin kasa da kasa.

Talla

A cikin wata sanarwa da ya aika ta kafar Twitter, Trump ya ce, tuni ya bayar da umarnin janye wasu karin takunkuman kan Korea ta Arewa.

Mai Magana da yawun shugaban na Amurka, Sarah Sanders ta ce, Trump na kaunar takwaransa na Korea ta Arewa, Kim Jong-un, abinda ya sa yake ganin babu bukatar sake kakawa kasar karin takunkuman karayar tattalin arziki.

Wannan na zuwa ne bayan shugabannin biyu sun gaza cimma matsaya a wata ganawa da suka yi a birnin Hanoi a 'yan makwannin da suka shude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.