VENEZUELA

Venezuela ta haramta wa Guaido rike mukamin siyasa

Gwmanatin Venezuela ta sanar da tube jagoran ‘yan adawar kasar Juan Guaido daga mukaminsa na shugaban majalisar dokoki, tare da hana shi rike duk wani matsayi a aikin gwamnati har tsawon shekaru 15 saboda samun sa da laifin rashawa.

Juan Guaido a zauren Majalisar Dokokin Venezuela
Juan Guaido a zauren Majalisar Dokokin Venezuela REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Babban mai binciken kudi na kasar Elvis Amoroso ne ya sanar da wannan mataki a birnin Caracas.

Elvis Amoroso wanda ke gabatar da taron manema labarai, ya ce Juan Guaido ya gaza bayyana in da yake samun kudaden da yake kashewa ta hanyar yin tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare.

Elvis ya ci gaba da cewa, Guaido ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya har sau 91, in da ya kashe kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka dubu 168.

A karkashin dokokin kasar ya zama wajibi ya yi wa ofishin mai bincike bayani dangane da in da yake samun wadannan kudade, rashin yin hakan kuwa, na nufin cewa Guaido na amfani da matsatsayin da ba nashi ba domin tattara kudade da sunan al’ummar kasar Venezuela, kuma hakan na a matsayin rashawa ne.

To sai dai Guaido ya yi watsi da wannan mataki, in da ya bayyana Elvis Amoroso a matsayin wanda ba shi da wani halasci a gaban doka, in da ya ce, yanzu haka majalisar dokokin kasar na shirin nada wani sabon mai bincike kan yadda ake kashe kudaden kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI