Turkiya

Jam'iyya mai mulki ta sha kashi a Turkiya

Wasu daga cikin masu kada kuri'u a Turkiya
Wasu daga cikin masu kada kuri'u a Turkiya REUTERS/Huseyin Aldemir

Jam’iyyar shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ta samu gagarumin koma-baya a zaben kananan hukumomi, in da ta sha kashi a hannun jam’iyyar adawa a manyan biranen kasar da suka hada da Ankara da Santanbul.

Talla

Ana kallon zaben na magadan-gari da shugabannin kananan hukumomi a matsayin gwajin-dafi ga jam’iyyar AKP ta shugaba Erdogan bayan da kasar ta tsindima cikin matsalar tattalin arziki a karon farko cikin shekaru 10.

Shugaban Hukumar Zaben Kasar, Sadi Guven ya bayyana cewa, dan takarar jam’iyyar adawa, Ekrem Imamoglu ya bai wa abokin hamayyarsa, Binali Yildirim tazarar kuri’u dubu 28 a zaben da aka gudanar a birnin Santanbul.

Imamoglu na da kuri’u kimanin miliyan 4.16, yayinda Yildirim da ya kasance tsohon Firaminista, ke da kuri’u miliyan 4.13.

Koda yake akwai akwatina 84 da kawo yanzu ba a kammala gidayar su ba a Santanbul din.

A can birnin Ankara kuwa, dan takarar jam’iyyar adawa, Mansur Yavas na kan gaba da kashi 50.89 na kuri’un da aka kada, in da abokin fafatawrsa daga jam’iyya mai mulki, Mehmet Ozhaseki ke da kashi 47.06, kuma an kidaya kimanin kashi 99 cikin 100 na jumullar kuri’un da aka kada a birnin.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyya mai mulki sun ce, ba za su amince da sakamakon ba saboda a cewarsu, akwai dubban kuri’un da aka soke a biranen na Ankara da Santanbul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.