MDD ta yi gargadi kan kyamar Musulmi a duniya
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da yadda matslar kyamar Musulmi ke dada kamari, kasa da wata guda da kaddamar da harin da ya kashe Musulmai 50 a wasu Masallatai da ke New Zealand.
Sakate Janar na Majalisar, Antonio Guterres ya yi gargadi a wani jawabi da ya gabatar a jami’ar Al-Azhar da ke Masar, in da ya gana da shugabanta, Sheik Ahmed al-Tayeb.
Guterres ya ce, duniya na fama da tsanantar matsalar kyamar Musulmi da kyamar Yahudawa da nuna wariyar launin fata har ma da kyamar baki.
Magatakardan ya tabo batun harin da wani mai rajin fifita farar fata ya kai a Masallatan New Zealand da kuma harin da aka kai wa Yahudawa a Majami’arsu da ke Pittsburgh, harin da aka bayyana a matsayin mafi muni kan Yahuwa a tarihin Amurka.
Guterres da ke ziyarar kwanaki biyu a Masar, zai gana da shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu