Saudiya

Saudiya ta rufe bakin iyalan Khashoggi da makuden kudade

Mahukuntan Saudiya sun bai wa ‘ya’yan shahararren marigayin dan jaridar kasar da aka yi wa kisan killa, Jamal Khashoggi kyautar gidajen kasaita, baya ga albashin dubban Daloli da za a ci gaba da biyan su a duk karshen wata.

Salah Khashoggi da Yarima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed bin Salman
Salah Khashoggi da Yarima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed bin Salman Handout / Saudi Press Agency / AFP
Talla

Jaridar The Washington Post da ta bankado labarin ta ce, matakin da Saudiyar ta dauka na yin ihsani ga ‘ya’yan marigayin da suka hada da maza biyu da mata biyu, na cikin yunkurin da take yi don ganin ta cimma wata yarjejeniya da iyalan Khashoggi da zummar hana su ci gaba da daukaka maganar kisan da aka yi masa.

Jaridar ta ce, darajar kudin gidajen da aka bai wa ‘ya’yan nasa a birnin Jeddah, ta kai Dalar Amurka miliyan 4, kwatankwacin Nairar Najeriya, biliyan 1 da miliyan 440.

Babban dan marigayin wato, Salah Khashoggi na da burin ci gaba da zama a Saudiya, amma sauran kannansa na da muradin ci gaba da rayuwa a Amurka, kuma ana sa ran za su sayar da gidajen da aka ba su a birnin na Jeddah kamar yadda jaridar ta The Washington Post ta rawaito.

Baya ga kyautar makuden dalolin da Masarautar Saudiyar za ta rika ba su a duk wata, har ila yau, za a yi musu wata kyautar miliyoyin Daloli na daban.

An dai zargi yarima mai jiran gadon Saudiya, Mohammed bin Salman da hannu a kisan Jamal Khashoggi, wanda aka yi gunduwa-gunduwa da namansa bayan kashe shi a ofishin jakadancin Saudiyar da ke birnin Santanbul na Turkiya a cikin watan Oktoba.

Sai dai Saudiya ta musanta cewa, Ibnu Salman ne ya kitsa hallaka dan jaridar da ke sukan lamirin gwamnatin kasar.

Tuni kasar ta tuhumi mutane 11 kan kisan marigayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI