Venezuela

Juan Guaido na tsaka mai wuya

Juan Guadió Dan adawar kasar Venezuela
Juan Guadió Dan adawar kasar Venezuela Fuente: Reuters.

A Venezuela madugun adawa dake ayyana kansa a matsayin shine shugaban kasar Juan Guiado ya fara shan jinin jikinsa cewa Hukumomin kasar na iya kama shi, bayan da Majalisar kasar ta cire masa rigar kariya da yake takama da ita kasancewar shine shugaban majalisar dokokin kasar.

Talla

Tsohon Shugaban Majalisar dokokin kasar ta Venezuela Juan Guiado ya fadi cewa tunda Hukumomin Venezuela suka sanar da sauke shi daga mukamin Shugaban Majalisa yanzu kam hukumomin kasar na iya sace shi.

Yau Laraba ,majalisar kasar ta sanar da cire masa rigar kariya.

Kasashen Duniya akalla 50 ya zuwa yanzu ke cewa shi suka sani a matsayin shugaban Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI