Bakonmu a Yau

Janar Martin Luther Agwai kan ranar wayar da kan jama’a dangane da illar dasa nakiyoyi a duniya

Sauti 03:36
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Denis Balibouse/File photo

A yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin wayar da kan jama’a dangane da illar dasa nakiyoyi a duniya.Tun kafa dokar hana mu’amala da nakiyoyi a shekara ta 1997, kasashen duniya 156 suka sanya hannu don amincewa da kafuwar dokar.Kan haka Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga Janar Martin Luther Agwai mai murabus wanda ya tafi yaki da dama a sassan duniya inda aka yi amfani da nakiyoyi ba kangado kuma mun nemi ji daga bakinsa, wasu daga cikin illolin dasa nakiya.