WHO-Lafiya

Wa'adin nisan-kwana ya karu a kasashen duniya

Kwallon duniya
Kwallon duniya geotests.net

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce, wa’adin nisan-kwana a duniya ya karu da kashi 5.5 cikin 100 tun daga shekarar 2000 zuwa 2016.

Talla

Rahoton Hukumar ya nuna cewa, a yanzu, yaron da aka haifa a shekarar 2016, ka iya rayuwa har tsawon shekaru 72, abinda ke nufin cewa, an samu karuwar wa’adin nisan-kwana da kashi 66.5 idan aka kwatanta da shekarar 2000.

Kididdigar rahoton ya bayyana cewa, an samu raguwar mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar musamman a yankin kasashen Afrika da ke kudu da sahara, in da aka samu ci gaba a yaki da cutar Malaria da Kyanda da sauran cutukan da ke yaduwa tsakanin jama’a.

Har ila yau, an samu karuwar wa’adin nisan-kwana a duniya saboda ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar Kanjamau wadda ta nakasa yankuna da dama a nahiyar Afrika a tsakankanin shekarar 1990.

Sai dai Hukumar Lafiyar ta Duniya ta gargadi cewa, rashin daidaiton samun kudaden shiga tsakanin al’umma da kuma kalubalen kula da lafiya, na haddasa karancin wa’adin nisan-kwana ga jama’a da dama.

Kazalika rahoton ya ce, akwai tazarar wa’adin nisan- kwana tsakanin kasashen duniya da suka ci gaba da kuma kasashe maso tasowa.

Rahoton ya bada misalin kasashen Lesotho da Afrika ta Tsakiya, in da wa’adin nisan-kwanan bai wuce shekaru 52 zuwa 53 ba, sabanin kasahen Switzerland da Japan in da wa ‘adin nisan-kwanan ya zarce shekaru 83 zuwa 84.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI