Venezuela

Juan Gaido na shirin kawo karshen mulkin Maduro

Juan Gaido dan adawa da gwamnatin Nicolas Maduro
Juan Gaido dan adawa da gwamnatin Nicolas Maduro Manaure Quintero / Reuters

Shugaban yan adawa na kasar Venezuela Juan Gaido a jiya asabar ya bayyana cewa ,ya kama hanya ko kuma shiga mataki na karshe don kawo karshen shugabancin Nicolas Maduro a kasar.

Talla

Magoya bayan shugaban yan adawa sun gudanar da zanga-zanga,inda Juan Gaido ya bayyana takaicin sa dangane da rashin wuta dama karancin kayakin more rayuwa da yan kasar ke fama da shi tsawon lokaci.

Juan Gaido ya bayyana cewa shirye yake ya kawo karshen mulkin Nicolas Maduro, yayinda Shugaba Maduro ya bayyana fatan sa na ganin kasashen Mexico da Uruguay ,Bolivia da wasu kasashen yankin Caraibe sun tsoma bakin su a batun sulhunta bangarorin biyu cikn dan karamin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI