Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta bukaci kawo karshen matakan soji a Libya

Wasu daga cikin sojojin da Khalifa Haftar ke jagoranta a Libya
Wasu daga cikin sojojin da Khalifa Haftar ke jagoranta a Libya ©REUTERS/Esam Omran Al-Fetori
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Amurka ta bukaci dakatar da matakan sojin da dakarun Khalifa Haftar suka kaddamar a Libya domin karbe iko da birnin Tripoli, bayan kiran tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta yi domin kwashe wadanda suka samu raunuka ya ci tura.

Talla

Yayin da yake bayyana matsayin gwamnatin Amurka, Sakataren Harkokin Waje, Mike Pompeo ya ce, sun bayyana karara cewar, suna adawa da daukar matakan soji daga bangaren Khalifa Haftar, in da suka bukaci dakatar da matakin ba tare da bata lokaci ba.

Pompeo ya ce, ta hanyar tattaunawa ce kawai za a iya magance rikicin Libya, kamar yadda Amurka da kawayenta ke bukatar ganin bangarorin da ke rikicin sun koma teburin tattaunawa.

Rahotanni sun ce, an samu hare-hare daga bangarorin biyu, abinda ya yi sanadiyar kashe mutane 21 da jikkata wasu da dama.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ya ziyarci kasar ya kuma gana da shugabannin bangarorin biyu, ya bayyana takaicinsa kan abinda ke faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.