India-pakistan

India na shirin kai sabon hari kan Pakistan

Pakistan ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya game da shirin India na kai mata hare-haren
Pakistan ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya game da shirin India na kai mata hare-haren World Defence Forum/Facebook

Ministar Harkokin Wajen Pakistan, Shah Mahmood Qureshi ya bayyana cewar sun samu bayanai masu karfi da ke nuna musu cewar, India na shirin kaddamar da hare- haren soji a cikin kasar nan gaba cikin wannan wata na Afrilu.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai, ministan ya ce, tuni suka sanar da Jakadun kasashen duniya da ke Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wannan shiri na India.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi kamari bayan da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ya hallaka jami’an tsaron India 40 a yankin Kashmir.

Sai dai kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen India, Raveesh Kumar ya yi watsi da zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.