Iran- Amurka

Amurka ce shugabar 'yan ta'addan duniya- Iran

Wasu daga cikin dakarun juyin juya halin Iran da Amurka ta ayyana a matsayin 'yan ta'adda
Wasu daga cikin dakarun juyin juya halin Iran da Amurka ta ayyana a matsayin 'yan ta'adda STRINGER / afp

Gwamnatin Iran ta bayyana Amurka a matsayin kasar da ke kan gaba wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta ayyana dakarun juyin juya halin Iran a matsayin kungiyar ‘yan ta’addan kasashen ketare .

A yayin mayar da martani, shugaban Iran Hassan Rouhani ya diga ayar tambaya kan Amurka, in da ya ce, “ wacece ita da har za ta ayyana rundunar dakarun juyin juya hali a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda?”

Rouhani ya bayyana cewa, Amurka ce shugabar ‘yan ta’adda a duniya.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Javad Zarif ya bukaci shugaba Rouhani da ya sanya Cibiyar Sojin Amurka a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta’adda na duniya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya bayyana cewa, sun dauki matakin sanya dakarun cikin jerin ‘yan ta’adda ne saboda yadda Iran ke daukar matakai daban-daban wajen taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Pmpeo ya ce, “wannan ne karo na farko da kasar Amurka ke bayyana wani sashe na gwamnati a matsayin mai taimaka wa ayyukan ta’addanci."

“Yanzu harkokin kasuwanci da kuma bankunan kasashen duniya na da hakkin da ya rataya akan su na ganin kamfanonin hada-hadar kudade sun daina duk wata hulda da rundunar Iran ta kowacce hanya.” A cewar Pompeo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.