Faransa- Amurka

Matakin Faransa kan haraji ya harzuka Amurka

Wakilan Majalisar Dokokin kasar Faransa na shirin fara muhawara dangane da sabon haraji kan manyan kafofin sadarwa na zamani da suka hada da Facebook da Apple, wanda hakan ya harzuka Amurka.

Zuren Majalisar Dokokin Faransa
Zuren Majalisar Dokokin Faransa GERARD JULIEN / AFP
Talla

Amurka ta roki Faransa da ta kasance aminiyarta a Kungiyar Tsaro ta NATO da ta jingine wannan batu na karin harajin, in da har Sakataren Waje na Amurkar, Mike Pompeo ke gargadi a makon jiya cewa, matakin zai shafi kamfanonin Amurka da Faransawa ke cin moriyarsu.

Dokar da Faransa ta kafa mai suna GAFA, in da ta dauko haruffan farko na Google, Amazon, Facebook da Apple na zuwa ne a wani lokaci da ake kokawa kan yadda wasu manyan kamfanoni na duniya ke biyan kudaden haraji kadan.

Ministan Kudi na Faransa ya ce, matakin da Faransa ta dauka na da nasaba da korafe-korafen da ake yi kuma ana ganin wakilan Majalisar Dokokin Faransan za su ci gaba da muhawara game da batun har zuwa ranar Laraba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI