Afghanistan

Taliban ta hana kungiyoyin agaji aiki a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta haramta wa kungiyoyin agaji da suka hada da Hukumar Lafiya ta Duniya gudanar da ayyukansu a Afghanistan. Tuni Kungiyar Agaji ta Red Cross ta dakatar da ayyukanta jim kadan da sanarwar ta Taliban.

Wasu daga cikin mayakan Taliban na Afghanistan
Wasu daga cikin mayakan Taliban na Afghanistan REUTERS/Parwiz
Talla

A cikin sanarwar da ta fitar, Taliban ta ce, Red Cross ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da mayakanta.

Kazalika mayakan na Taliban da ke rike da kusan rabin kasar ta Afghanistan, sun zargi Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da nuna wani irin taku a yayin gudanar da aikinta na yi wa jama’a riga-kafin cutuka, takun da Taliban ta ce, sam bata gamu da shi ba.

Wadannan dalilan ne suka tilasta wa Taliban hana kungiyoyin biyu gudanar da ayyukansu a fadin kasar har sai baba-ta-gani, yayinda mayakan ke cewa, ba za su iya tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatan Red Cross da na WHO ba.

A martanin da ta mayar, Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bakin kakinta, Robin Waudo, ta ce, ta dakatar da ayyukanta a Afghanistan mai fama da rikici duk da cewa, akwai dimbin jama’a da ke cikin matsananciyar bukatar agajin Red Cross musamman a yankunan karkara da ke fama da cutar shan-inna.

Red Cross ta ce, a halin yanzu, tana kan tuntubar Taliban domin tattaunawa da ita game da wannan sanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI