Seychelles

Shugaban Seychelles ya yi jawabi ga duniya daga karkashin teku

Shugaban Seychelles, Danny Faure jim kadan da fitowarsa daga karkashin tekun India
Shugaban Seychelles, Danny Faure jim kadan da fitowarsa daga karkashin tekun India France24

Shugaban kasar Seychelles, Danny Faure wanda ke tare da tawagar wasu masana da yanzu haka ke gudanar da aikin bincike a karkashin tekun India, ya ce abinda ya gane wa idanuwansa a karkashin tekun na matukar tayar da hankula, musamman yadda matsalar gurbatar yanayi ke ci gaba da yin mummunan ta’addi ga ruwan tekun.

Talla

A jawabin da ya gabatar daga karkashin tekun, shugaba Faure ya ce ya zama wajibi duniya ta dauki matakan gaggawa kan wannan matsala.

A jawabin nasa shugaban y ace, “ A yau na samu damar kasancewa karkashin ruwan teku har tsawon mita 124, tabbas ruwan teku na da alaka ta kai-tsaye da dukkaninmu, teku na taka rawa domin tabbatuwar halittun da ke duniya na raye ciki har da dan adam.”

“Abin da na gane wa idanuwana, na nuni da cewa teku na fuskantar babbar barazanar da bai taba cin karo da makamanciyarta ba a tarihi, alhali kuwa teku ne ke samar da rabin tsaftaccen numfashin da muke shaka, tare da zuke sama da kashi 30% na gurbatacciyar iskar da duniya ke fitarwa.” In ji shugaba Faure

Shugaban daga can karsashin ruwa, ya kara da cewa, “Rahoto na baya-bayan nan ya tabbatar da cewa teku na samar wa tattalin arzikin duniya akalla Dala triliyan 24, to amma bai kamata a ci gaba da gurbata ruwan teku don habaka tattalin arziki ba, domin kuwa amfaninsa wajen kare lafiyar dan adam shi ne ya kamata a bai wa muhimmanci.”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI