Bakonmu a Yau

Dr Abdullahi Kauran-Mata kan bazuwar cutar kyanda a sassan duniya

Wallafawa ranar:

Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da barkewar cutar Kyanda a sassan duniya cikin watanni uku da suka gabata kuma bayanai na nuna cutar na kara bazuwa kamar wutar daji a kasashen duniya.Rahoton na nuna akasar Amurka inda tafi kamari mutane akalla 555 suka kamu cikin watanni uku da suka gabata. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Abdullahi Kauran-mata na Asibitin Aminu Kano Najeriya, ko me ya haifar da wannan annoba yanzu.

Tawagar Jami'an lafiya da ke rigakafin cutar kyanda a Somalia
Tawagar Jami'an lafiya da ke rigakafin cutar kyanda a Somalia WHO