Amurka-Rasha

Majalisa ta yi sammacin bankuna kan badakalar Trump da Rasha

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque

‘Yan Majalisun Amurka na Jam’iyyar Democract sun amince da mika sammaci ga wasu bankuna ciki har da bankin Deutsche don bayyana gaban kotu da shaidu game da zargin badakalar kudin da ake kan shugaban kasar Donald Trump yayin zaben 2016.

Talla

Sammacin wanda shugaban kwamitin binciken kudi na Majalisar Dokokin Amurka Adams Schiff ke sanarwa jiya Talata, ya ce ta hakanne kawai za su bankado gaskiyar zargin da ake yiwa Donald Trump kan badakalar wasu tarin kudi da suka kai ga kutsen Rasha a zaben kasar na 2016.

Cikin bankunan da Majalisar Amurkan ta aikewa sammacin har da bankin Deutsch wanda ya bayar da bashin kudin da aka yi ginin Trump real estate, tun a shekarar 1990.

Cikin jawaban da Mr Schiff ya gabatar gaban zaman Majalisar, ya ce ta hanyar gayyatar bankin na Deutsch ne kadai za a fayyace gaskiyar badakalar kudaden da Trump ya aikata tsakan-kanin kasashen Turai yayin zaben kasar, wanda kawo yanzu Shugaban ke ci gaba da musantawa.

Aikewa da takardun sammacin ga bankunan duniya, na zuwa ne kwanaki 2 kafin sakin wani rahoto na musamman da Majalisar ta shafe shekara biyu ta na bincike kan sa, dangane da zargin kutsen Rasha a zaben kasar.

Sai dai fa, ko a watan jiya, wani binciken babban mai shari’a a Amurkan Bill Barr ya gano cewa babu wata alaka tsakanin shugaban mai ci Donald Trump da Moscow yayin zaben na 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.