Peru

Tsohon shugaban kasa ya kashe kansa da bindiga

Tsohon shugaban kasar Peru, Alan Garcia ya dirkawa kansa bindiga a ka, lokacin da ‘yan sanda suka je kama shi a gidansa, saboda tuhumar da ake masa ta cin hanci da rashawa.

Tsohon shugaban Peru da ya kashe kansa, Alan Garcia
Tsohon shugaban Peru da ya kashe kansa, Alan Garcia REUTERS/Tim Chong
Talla

Jam’iyyar (Apra ) ta tsohon shugaban, ta tabbatar da mutuwarsa a asibiti.

Ministan Lafiya na kasar, Zulema Tomas, ya ce, sau uku likitoci na farfado da Garcia bayan ya gamu da bugun-zuciya a daidai lokacin da ake yi masa tiyatar harbin bindigar, amma daga bisani ya sheka lahira.

Garcia da ya mulki Peru tsakanin shekarar 1985-1990 da kuma 2006-2011, na fuskantar tuhumar karbar cin hanci daga kamfanin gine-gine na Brazil, Odebretch , yayinda a cikin watan Nuwamba ya nemi mafakar siyasa a ofishin jakadancin Uruguay bayan kotu ta hana shi ficewa daga kasar har tsawon watanni 18.

Kodayake daga bisa Uruguay ta hana shi mafakar bayan shafe kwanaki 16 a ofishin jakadancinta.

Jami’an ‘yan sandan sun ziyarci gidansa ne bayan sammacin da suka samu na kama shi kan zargin almundahana, matakin da ka iya sa a tsare shi har tsawon kwanaki 10 domin kammala bincike a kansa.

Shugaban kasar Peru, Martin Vizcarra ya bayyana damuwarsa kan mutuwar Garcia tare da mika sakon ta’aziya ga iyalansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI