Amurka

Trump ya yi kokarin hana gudanar da bincike a kansa

A yayinda shugaban Amurka Donald Trump ke murnar samun nasarar kubuta daga zargin katsalandan din Rasha zaben 2016, wasu bayanai na cewa, shugaban ya yi kokarin karbe iko da gudanar da binciken a can baya, tare da yunkurin tsige lauyan da ke aikin gudanar da binciken.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

Rahoton lauyan nan na musamman Robert Mueller, ya bayyana cewa, a shekarar 2017, shugaba Trump ya umarci lauyan Fadar White House, Don McGahn da ya zanta da mukaddashin mai shigar da kara na gwamnati ta wayar ta tarho kan yadda za a tsige Mueller saboda banbanci ra’ayinsa da nasu.

Sai dai lauyan na Fadar White ya yi kunnen kashi da umarnin Trump, in da ya zabi ajiye aikinsa a maimakon aiwatar da umarnin da ya bayyana a matayin kisan-kare dangi.

Rahoton Mueller ya bayyana cewa, shugaba Trump ya shiga cikin tashin hankali a farko farkon kaddamar da binciken, in da har yake cewa, karshen mulkinsa ya zo.

A jiya Alhamis ne, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta wallafa tataccen rahoton na Mueller a shafin intanet, bayan mintina 90 da Mai Shigar da Kara na Gwamnatin kasar, William Barr ya gabatar da nasa fashin bakin sakamakon rahoton.

Sai dai manazarta sun diga ayar tambaya game da matakan Trump, suna masu cewa, masu binciken ba su wanke shugaban daga zargin kokarin hana gudanar da shari’a ba.

Tuni dai shugaban na Amurka ya ce, yana cikin annashuwa saboda komai ya zo karshe a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI