Syria-IS

IS ta hallaka sojin Syria 50 cikin mako 2

Wani yanki da mayakan IS suka farmaka a Syria
Wani yanki da mayakan IS suka farmaka a Syria REUTERS/Stringer

Akalla sojojin Syria 50 mayakan IS suka hallaka a sassa daban-daban na kasar cikin sa’o’i 48 yayin hare-haren da bangaren mayakan da kuma ‘yan tawaye suka tsananta kai wa kansu a cikin makwannin baya-bayan nan.

Talla

Cikin watan Maris ne dai mayakan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka suka shelanta murkushe mayakan na IS bayan farmakar maboyarsu ta karshe, sai dai da alama sabbin hare-haren na nuni da cewa mayakan sun samu wata sabuwar maboya a kasar ta Syria.

Hukumar kare hakkin dan adam da ke sanya idanu a rikicin kasar ta ce daga Alhamis din da ta gabata zuwa yau akalla sojojin Syrian 35 ne suka kwanta dama sanadiyyar hare-haren IS.

Rami Abdel Rahman, ya ce adadin mayakan na Syria da aka hallaka cikin makon nan shi ne adadi mafi muni da aka samu tun bayan fatattakar mayakan na IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI