Amurka-Rasha

Democrat ta sha alwashin daukar matakin tsige Donald Trump

Adam Schiff
Adam Schiff Reuters

Jam’iyyar Democrat a Amurka ta ce nan gaba kadan za ta yanke hukunci ko daukar matakin tsige shugaba Donald Trump zai yiwa Amurka tasiri ko kuma a’a.

Talla

Shugaban kwamitin leken asiri a Majalisar wakilai, Adam Schiff, ya ce tunda Jam’iyyar Republican ke da rinjaye a Majalisar Dattawa zai yi wahala wajen samun goyan bayan da ya dace dangane da shirin, duk da shaidu guda 10 da ake da su a rahotan binciken Robert Mueller.

Rahoton binciken na Robert Mueller dai ya fito karara ya nuna yadda shugaba Donald Trump ya taka rawa wajen katsalandan lokacin gudanar da binciken.

Dan majalisar ya ce rashin daukar wannan mataki zai nuna cewar abinda shugaba Trump yayi daidai ne, kuma wasu shugabanni masu zuwa nan gaba suma suna iya yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.